Yanzu Yanzu: Dalilin da yasa muka kai mamaya gidan gwamnatin Ekiti – Yan sanda

Yanzu Yanzu: Dalilin da yasa muka kai mamaya gidan gwamnatin Ekiti – Yan sanda

Rundunar yan sandan jihar Ekiti a ranar Laraba, 11 ga watan Yuli sun mamaye gidan gwamnatin jihar, inda suka hana shige da fice tare da jami’ansu dauke da kayayyakin aiki da motocin Hilux.

Wasu jami’an yan sanda da adadinsu ya kai sama da 50 sun toshe hanyar shiga gidan gwamnatin jihar Ekiti, inda suka hana shige da fice a gidan.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa wani moton yaki na yan sanda da motocin hilux sun paka a mashigin gidan inda suka toshe hanyar da zai sada yankin da ofishin Gwamna Ayodele Fayose.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Ekiti, Caleb Okechukwu ya fadama manema labarai cewa an zuba yan sanda a gidan gwamnati ne domin su tsare dukkanin jama’a. “Aikinmu ne bayar da tsaro ga kowa sannan kuma shine abunda meke kan yi,” inji Okechukwu.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Jami’an tsaro sun tarwatsa magoya bayan PDP daga wajen gangami

Da aka tambaye shi ko hana shige da ficen na gidan gwamnatin don kare gwamnan ne, kawai Okechukwu ya bayyana cewa an zuba yan sanda domin kare jama’a ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel