Kotu ta bayar da umarin garkame shuwagabannin jam'iyyar PDP 2 a gidan kurkuku

Kotu ta bayar da umarin garkame shuwagabannin jam'iyyar PDP 2 a gidan kurkuku

- Wasu shugabannin PDP sun gamu da fushin kuliya

- Tun farko dai hukumar EFCC ce ta fara cafke sannan ta gurfanar da su gaban alkali

- Bayan rokar belinsu ta bakin lauyansu, alkalin yayi kemadagas ya hana

A jiya ne alkalin wata kotun tarayya dake zamanta a garin Legas, Sule Hassan ya bada umarnin cigaba da tsare shugaba da kuma kakakin yakin neman zaben jam'iyyar PDP na jihar Ondo, Clement Faboyede da Modupe Adetokunbo a gidan kaso har sai ranar 19 ga watan Yuli.

Kotu ta bada umarnin tsare shuwagaban jam'iyyar PDP a gidan kurkuku

Kotu ta bada umarnin tsare shuwagaban jam'iyyar PDP a gidan kurkuku

An dai kama Clement da Adetokunbo ne tun ranar 29 ga watan Yunin da ya gabata, wanda hukumar hana cin hanci da rashawa ta kama su bisa laifin yin sama-da-fadi da kudi kimanin milyan 500.

KU KARANTA: Wasu jam'iyyu 20 sun hada gwuiwa da APC domin marawa Buhari baya

Bayan gurfanar da su gaban kotun a ranar 29 ga watan da ya gabata ne mai Shari'ah Said ya bada umarnin tsare su har 19 ga watan Satumba sannan ne za a cigaba da sauraren shari'ar.

Bayan sauraren neman bukatar bada belinsu a jiya, mai Shari'ar ya ba da umarnin cigaba da tsare su har zuwa 19 ga watan Yuli, kafin aka kawo shaida da kuma shaidar cika ka'idar belin nasu.

Lauyan nasu jim kadan bayan gama zaman kotun ya bayyana cewa "Maƙasudin wannan bukata shi ne kotu ta bada belinsu na wani lokaci tunda ba a yanke musu hukunci ba. Duk da cewar hukumar EFCC ta amince da a bada belin nasu, muna fatan kotun zata musu sassauci wajen ganin an bayar da su ba tare da samun tsaiko ba".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel