Alkalai na samun barazana daga gwamnatin Buhari gabanin zabe - Obasanjo

Alkalai na samun barazana daga gwamnatin Buhari gabanin zabe - Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya zargi shugaba Muhammadu Buhari da yiwa Alkalai barazana saboda su mara wa jam'iyyarsa ta APC baya game da harkokin zabe.

Obasanjo dai ya huro wuta cikin yan kwanakin nan inda yake sukar shugaba Buhari kan ya yi watsi da batun sake tsayawa takara a 2019. Ya kuma yi ikirarin cewa Buhari na amfani da hukumomin yaki da rashawa wajen musgunawa yan adawa.

Obasanjo ya yi wannan maganar ne a Abuja wajen wata liyafa da aka shirya don murnar cika shekaru 70 na tsohuwar Ministan mata da cigaban al'umma, Josephine Anenih.

Gwamnatin APC na yiwa Alkalai barazana gabanin zaben 2019 - Obasanjo

Gwamnatin APC na yiwa Alkalai barazana gabanin zaben 2019 - Obasanjo

DUBA WANNAN: Ina nan a Jam'iyyar APC daram dam - Gwamna Ortom

"Gwamnati na amfani da hukumomi da aka kafa don tabbatar da gaskiya kamar su EFCC, ICPC, FIRS da Ma'aikatar shari'a na kasa wajen musgunawa abokan hammaya," inji shi.

"An fara amfani da karfin bindiga a wasu jihohin. An gano cewa an fara yiwa wasu Alkalai barazana saboda a tsorata su don su zama 'yan korar gwamnati mai mulki. Dukkan wadannan abubuwan na faruwa ne a demkradiyar Najeriya.

Duk da cewa tsohon shugaban kasan bai bayyana sunayen wadanda yace ana yiwa barazanar ba, ya sake jadada cewa dimokradiyya ta tsari ce dake bawa kowa ikon fadin albarkacin bakinsa saboda gwamnti ce ta mutane.

Obasanjo kuma ya yi tsokaci kan yadda gwamnati bata damawa da mata wajen basu mukammai da damar fitowa takarar wasu kujeru. Ya ce gwamnatin Buhari bata cika ka'iddar guraben da aka ware wa mata a gwamnati ba.

Hakan yasa ya yi kira ayi gyra a kundin tsarin mulkin 1999 don a mayar dashi doka cewa dole mata su cike gurabe 40% a gwamnati.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel