Ikon kwace kadarori: Dalilin da ya sa zamu raba Shugaban kasa da ikonsa - Majalisa

Ikon kwace kadarori: Dalilin da ya sa zamu raba Shugaban kasa da ikonsa - Majalisa

Majalisar wakilai za ta mayar da ikon kwace kadarorin masu laifi daga hannun Shugaban kasa, Muhammad Buhari zuwa ga Alkalan manyan kotunan kasar.

Shugaban majalisar, Yakubu Dogara ya ce sun yanke wannan shawara ne domin hakan zai karfafawa bangarorin gwamnati ta yadda za su gudanar da ayyukansu kamar yadda tsarin mulki ya tanada tare kuma kara baiwa tsarin dimokradiyya gindin zama.

Ikon kwace kadarori: Dalilin da ya sa zamu raba Shugaban kasa ikonsa - Majalisa

Ikon kwace kadarori: Dalilin da ya sa zamu raba Shugaban kasa ikonsa - Majalisa

Sai dai wasu na ganin wannan mataki da majalisar ke shirin dauka bai rasa nasaba da " umarnin Shugaba na musamman " na kwace kadarorin da aka mallaka da kudaden rashawa wanda Buhari ya rattaba hannu a kai kwanan nan.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa kasa da sa’o’i 24 bayan babban jam’iyyar adawa, Peoples Democratic Party (PDP), da sauran jam’iyyun siyasa 34 sun kullaa yarjejeniyar fahimta don kwace mulki daga jam’iyyar APC mai mulki, wasu jaam’iyyu a jerin PDP sun nisanta kansu daga jam’iyyar Maja.

KU KARANTA KUMA: Babu wani hadin gwuiwa da zai hana Buhari lashe zaben 2019 - Minista

A ranar Litinin, jam’iyyun siyasa 39 sun kulla yarjejeniya domin fitar dad an takara guda a zaben 2019.

Jam’iyyun siyasar karkashin jam’iyyar Coalition of Unity Political Parties (CUPP) sun yanke shawarar shiga rantsuwa da mutanen Najeriya ta hanyar fara aiki a yayin mahawara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel