Bana nadamar tsigeni daga mukamina da aka yi

Bana nadamar tsigeni daga mukamina da aka yi

Tsohon kakakin majalisar Jihar Filato da aka tsige a yau Laraba 11 ga watan Yuli, Mr Peter Azi, yace bashi da wata nadama game da tsige shi da akayi.

Yan majalisar jihar sun tsige Azi dake wakiltan Kudu maso gashin Jos a zaman da majalisar tayi a ranar Laraba.

An kuma maye gurbinsa da Mr Joshua Madaki daga yankin Gabashin Jos ba tare da bata lokaci ba.

A yayin da yake zantawa da manema labarai, Azi yace tsige shi da akayi ba wani abin mamaki bane dama haka demokradiyya ta gada.

Bana nadamar tsigeni daga mukamina da aka yi

Bana nadamar tsigeni daga mukamina da aka yi

"A halin yanzu, bani nadamar tsigeni da kayi a matsayin kakakin majalisa a jihar Filato.

DUBA WANNAN: Ai shugaba Buhari ba zai sanya ayi kashe-kashe ba - Gowon

"Dama haka harkar mulki take, kawai na dauke shi a matsayin wata abu ne dake iya taimakawa wajen karfafa demokradiyar mu.

"Maganar gaskiya, an sauke min nauyi domin yanzu zan samu lokaci sosai don ganawa da mutanen mazabata saboda a matsayin kakakin majalisar na dauki dukkan jihar a matsayin mazaba ta.

"Nayi murna yadda abokan aiki ne basu fadi wani abin aibi cikin mulki na ba kawai dai sunce suna bukatar canjin shugabanci ne," inji shi.

Da aka tambaye shi ko yana ganin 'yan majalisar sun tsige shi ne saboda yana kare gwamna Lalong, Azi ya amsa da cewa, "idan wannan ne matsalar su basu fadi ba.

Ya kuma kara da cewa ai mutanen jihar da suka zabi yan majalisar ne suka zabi gwamna Simon Lalong.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel