Yanzu Yanzu: Kotu ta dage sauraron shari’ar bayar da belin Zakzaky zuwa watan Agusta

Yanzu Yanzu: Kotu ta dage sauraron shari’ar bayar da belin Zakzaky zuwa watan Agusta

Babban kotun jihar Kaduna ta dage sauraron shari’a kan bayar da belin shugaban kungiyar Shi’a, Sheikh Zakzaky.

Kotu ta sa ranar 2 ga watan Agusta a matsayin ranar ci gaba da shari’an bayan gwamnatin jihar Kaduna ta gurfanar da Zakzaky da matarsa Zeenat a ranar Laraba, 11 ga watan Yuli.

Ana tuhumar shugaban shi’an da matarsa da laifuka takwas wadanda suka hada da taro ba bisa ka’ida ba, tada zaune tsaye da sauran zarge-zarge.

Yanzu Yanzu: Kotu ta dage sauraron shari’ar bayar da belin Zakzaky zuwa watan Agusta

Yanzu Yanzu: Kotu ta dage sauraron shari’ar bayar da belin Zakzaky zuwa watan Agusta
Source: Depositphotos

An fara gurfanar da su a ranar 15 ga watan Mayu, 2018 inda kotu ta dage zaman kan bayar da belin su zuwa ranar 21 ga watan Yuni.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa nake son sake mulkar Ekiti - Fayemi

Sai dai ba’a samu damar zaman ba kamar yadda aka shirya saboda rashin zuwal alkali sannan aka dage zaman zuwa yau, domin ci gaba da shari’an.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel