Dalilin da ya sa nake son sake mulkar Ekiti - Fayemi

Dalilin da ya sa nake son sake mulkar Ekiti - Fayemi

Kayode Fayemi, dan takarar gwamna karkashin jam’iyyar APC a zaben Ekiti da za’a yi a ranar, Asabar ya ce yana so ya sake mulkar jihar ne domin rage talauci a tsakanin mutane.

Ya bayyana hakan ne a gangamin karshe da APC ta yi gabannin zaben a filin wasa na Oluyemi Kayode dake Ado Ekiti a ranar Talata, 10 ga watan Yuli.

Mista Fayemi wadda ya yi gwamnan jihar daga 2010 zuwa 2014, ya bayyanawa taron jama’a cewa magajinsa, Gwamna Ayodele Fayose, ya muzgunawa jama’ar jihar ta hanyar kin biyan albashi da fansho.

A cewarsa, da gangan Mista Fayose ya hana ma’aikatan gwamnati, malamai da yan fansho albashinsu na watanni takwas, kudin fansho da hakokinsu, saboda yana so ya horar da su sannan su fara bara a tituna.

Dalilin da ya sa nake son sake mulkar Ekiti - Fayemi

Dalilin da ya sa nake son sake mulkar Ekiti - Fayemi

Ya yabawa mutanen Ekiti da suka fito suka yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari barka da zuwa sabanin umurnin da gwamnan yayi na cewa kada wanda ya fito domin yiwa shugaban kasar maraba a jihar.

KU KARANTA KUMA: Sa’o’i 24 bayan shiga yarjejeniya, PDM, da wasu 19 sun nisanta kansu da Maja

Mista Fayemi wanda ya ajiye aiki a matsayin ministan ma’adinai don takara ya roki masu jefa kuri’u a jihar da su fito kwansu da kwarkwatansu a ranar Asabar domin su zabe shi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel