Wasu jam'iyyu 20 sun hada gwuiwa da APC domin marawa Buhari baya

Wasu jam'iyyu 20 sun hada gwuiwa da APC domin marawa Buhari baya

Kasa da sa'o'i 24 bayan jam'iyyar PDP da wasu jam'iyyu fiye da 30 sun hada gwuiwa domin goyawa dan takara guda baya, jam'iyyar APC ta hada gwuiwa da wasu jam'iyyu 20 domin goyawa takarar shugaba Buhari baya.

Da yake magana amadadin ragowar jam'iyyun da suka hada gwuiwa da APC, shugaban jam'iyyar PDM, Ibrahim, ya bayyana cewar hadakar PDP da wasu jam'iyyu damfara ce kawai ake so a yiwa 'yan Najeriya.

Wasu jam'iyyu 20 sun hada gwuiwa da APC domin marawa Buhari baya

Wasu jam'iyyu 20 sun hada gwuiwa da APC domin marawa Buhari baya

Kazalika ya bayyana cewar sun farfado da hadakar su ne da APC, wacce suka fara yi tun 2014, bayan ganin yaudarar da PDP ke kullawa.

DUBA WANNAN: 'Yan adawa na bata suna na da rikicin makiyaya da manoma

Ibrahim ya kara da cewar, "tun kafin a je ko ina wasu jam'iyyu da aka ambaci sun hada gwuiwa da PDP sun fito sun karyata shiga wata hadaka da jam'iyyar. Tuni dama muna da shakku a kan hadin gwuiwar da PDP ke ikirarin ta yi da jam'iyyu."

Da yawan 'yan Najeriya sun soki hadakar ta PDP da wasu jam'iyyu, suna masu bayyana hakan da hadin gwuiwa domin karbar mulki ta kowanne hali ba tare da wata manufa da zata inganta rayuwar mutanen Najeriya ba.

A nasa jawabin, sakataren hadakar jam'iyyu 20 da APC kuma Shugaban jam'iyyar APDA, Shitttu Muhammed Kabiru, ya bayyana cewar hadakar su ta goyon bayan dimokradiyya mai ma'ana ce tare tabbatar da gyaran tattalin arzikin Najeriya da PDP ta rusa lokacin da take kan mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel