Babu wani hadin gwuiwa da zai hana Buhari lashe zaben 2019 - Minista

Babu wani hadin gwuiwa da zai hana Buhari lashe zaben 2019 - Minista

Ministan Kwadago na kasa, Chris Ngige, yace babu wata irin taron dangi da zai hana shugaba Muhammadu Buhari lashe zabe a shekarar 2019. Ngige ya furta wannan magana ne a jiya a garin Ado Ekiti wajen yakin neman zaben Dr. Kayode Fayemi.

Yace taron dangin da wasu shugabani su keyi don kayar da shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019 ba zai yi tasiri ba saboda shugaban kasar ya kawo cigaba sosai a tattalin arzikin Najeriya idan aka kwatanta da halin da ya tsinci kasar a 2015.

Babu wani hadin gwuiwa da zai hana Buhari lashe zaben 2019 - Minista

Babu wani hadin gwuiwa da zai hana Buhari lashe zaben 2019 - Minista

Ya ce jam'iyyar ta APC wadda ta fara a matsayin Action Congress kafin daga baya ta canja suna zuwa APC ta kasance tana cigaba a kan turbar ta na kawo cigaba da inganta rayuwar yan Najeriya.

DUBA WANNAN: Ina nan a Jam'iyyar APC daram dam - Gwamna Ortom

Ngige ya shawarci mutanen jihar Ekiti suyi amfani da basira wajen zaben ta hanayr jefawa Dr, Kayode Fayemi kuri'arsu a ranar Asabar mai zuwa don su dare kan jirgin cigaba.

A cewarsa, jam'iyyun da suke hadin gwuiwa don ganin su kayar da shugaba Muhammadu Buhari suna bata loakcinsu ne don babu abinda zai hana shugaba Buhari lashe zaben.

"Duk taron dangin da ake yiwa shugaba Buhari ba zaiyi tasiri ba domin zai yi nasara, a baya jam'iyyun adawan sunyi hadin gwiwa don kayar dashi amma hakan baiyi tasiri ba.

"Ina mai tabbatar maka cewa wannan hadin gwiwar ma ba za tayi tasiri ba, wanda suke cewa zai fadi suna tsoro ne saboda za'a tilasta musu dawo da kudaden da suka sace," inji shi.

Ya kuma zargin gwamna Fayose da jefa mutanen jihar cikin bakar fatara da talauci, musamman yan kabilar igbo saboda rashin biyan albashin ma'aikata. Ya ce rashin biyan albashin na kawo cikas ga kasuwancin a jihar amma idan aka zabi Fayemi zai kawo gyara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel