Ina nan a Jam'iyyar APC daram dam - Gwamna Ortom

Ina nan a Jam'iyyar APC daram dam - Gwamna Ortom

A jiya Talata, Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue yace har yanzu yana nan a jam'iyarsa ta APC kana ya karyata rahotannin dake yawa a wasu kafafen yadda labarai dake cewa yana shirin sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP.

Wasu kafafen yadda labarai sun wallafa cewa Ortom yana shirin ficewa daga APC domin ya sake tsayawa takarar gwamna karo na biyu karkashin wata jam'iyyar.

Sai dai a yayin da ya yi hira da manema labarai a gidan gwamnati dake Makurdi, Ortom ya karyata rahotannin da kafafen yadda labaran suka wallafa.

Ina nan daram-dam a jam'iyyar APC - Gwamna Ortom

Ina nan daram-dam a jam'iyyar APC - Gwamna Ortom

DUBA WANNAN: Da Azikiwe yana raye tabbas zai goyawa Buhari baya

Yace gwamnatinsa ta sallame kwamishinoninsa da wasu 'yan fadarsa ne saboda a kawo wasu masu sabbin tunani cikin gwamnatin kuma za'a cigaba da yin hakan lokaci zuwa lokaci.

Gwamnan ya karyata cewa yayi korar ne saboda ya tsige wasu wanda basu goyon bayansa inda ya kara da cewa har wasu na kusa dashi abin ya shafe su.

A wata labarin mai alaka da wannan, mai kula da kungiyar magoya bayan Ortom 'I stan with Ortom' Kwamared Dan Nyikwagh ya yabbawa gwamnan saboda canjin da ya yi na ma'aikatan.

Nyikwagh ya bawa gwamnan shawara ya kawo sabbin hannu wanda zasu taimaka masa wajen cinma burinsa na kawo cigaba a jihar Benue.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel