Zaben jihar Ekiti: Za a jibge jami’an NSCDC 19,997 da na’urorin duba ababen hawa da kuma Karnukan masu ban tsoro

Zaben jihar Ekiti: Za a jibge jami’an NSCDC 19,997 da na’urorin duba ababen hawa da kuma Karnukan masu ban tsoro

- Ana cigaba da daukar tabbatar da tsauraran matakan tabbatar da tsaro a jihar Ekiti

- Hakan ya biyo bayan sake kusantowar zaben gwamnan jihar da za'a gudanar a karshen mako

- Wannan ta sanya hukumomin tsaro daban-daban suke ta jibge jami'ansu ciki ha da NSCDC

Babban kwamandan rundunar tsaron farin kayan ta NSCDC, Abdullahi Muhammadu ya bayar da umarnin kai jami'an rundunar kusan duba ashirin zuwa jihar Ekiti gabannin zaben gwamnan da za'a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.

Zaben jihar Ekiti: Za a jibge jami’an Civil Defence 19,997 da na’urorin duba ababen hawa da kuma Karnukan masu ban tsoro

Zaben jihar Ekiti: Za a jibge jami’an Civil Defence 19,997 da na’urorin duba ababen hawa da kuma Karnukan masu ban tsoro

Jami'an wadanda wadanda za su isa jihar ta Ekiti cikin cikakken shirin ko ta kwana su na tare da karnuka masu sunsunar abubuwan fashewa da kuma sauran ingantattun kayan aiki.

Ya bayar da wannan umarnin cikin wata sanarwa da kakakin rundunar na kasa DCC Emmanuel Okeh ya rabawa manema labarai a ranar Talata, a birnin Abuja.

Sanarwar ta kara da cewa wannan sanarwar ta zo a lokacin da babban kwamandan ya ke baiwa mataimakinsa mai kula da gudanar da aikace-aikace Hilary Madu Kelechi umarnin samar da isassun jami'an hukumar domin samar da tsaro gabanin da kuma bayan zaben.

KU KARANTA: Wuya tayi wuya: 'Yan Boko Haram sun tsere sun bar wata yarinya Sojoji sun ceto ta

Ya kuma bayyana cewa jami'an rundunar da za su yi wannan aikin sun hada da jami'an da ke jihohin Osun, Kogi, Edo, Ondo da kuma jihar Kwara.

Zaben jihar Ekiti: Za a jibge jami’an Civil Defence 19,997 da na’urorin duba ababen hawa da kuma Karnukan masu ban tsoro

Zaben jihar Ekiti: Za a jibge jami’an Civil Defence 19,997 da na’urorin duba ababen hawa da kuma Karnukan masu ban tsoro

"Bayan samar da wannan rundunar jami'an tsaron ta farin kaya, akwai kuma Mataimakan kwamandojojin tare da manyan jami'an rundunar wadanda za su taimaka wajen tabbatar da tsaro a fadin jihar ta Ekiti" in ji DCC Emmanuel Ikeh.

A karshe ya gargadi jami'an rundunar da su kauracewa dukkanin wani abu da ya sabawa doka ko rashin da'a, wanda dalilin hakan zai sa a hukunta wanda ya aikata hakan. Sannan ya kuma bukaci jami'an rundunar da su zama jakadu nagari ga rundunar ta su a lokacin da su ke gabatar da aikinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel