Duk karya ce: Har yanzu Buhari bai biya ko sisi ba na aikin titin jirgin kasan Abuja

Duk karya ce: Har yanzu Buhari bai biya ko sisi ba na aikin titin jirgin kasan Abuja

Babban kamfanin nan na fasahar kere-kere daga kasar China da ke aikin shimfida titin jirgin kasan zamani na cikin garin Abuja watau China Civil Engineering Construction Corporation ya ce har yanzu gwamnatin tarayya bata biya su kudin aikin su ba.

Mahukuntan kamfanin dai sun bayyana cewa aikin na su da suke yi tun a shekarar 2007, yana shan matsala daga bangaren gwamnati domin kuwa har yanzu ba'a biya su kudin su.

Duk karya ce: Har yanzu Buhari bai biya ko sisi ba na aikin titin jirgin kasan Abuja

Duk karya ce: Har yanzu Buhari bai biya ko sisi ba na aikin titin jirgin kasan Abuja

KU KARANTA: Kotu ta kwace Naira biliyan 2 ta wani tsohon hafsan soji

Legit.ng dai ta samu cewa titin mai tsawon murabba'in kilomita sama da 45 da ya kewaya cikin garin na Abuja shugaba Buhari zai kaddamar da shi ne a ranar Alhamis mai zuwa.

A wani labarin kuma, Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma mai neman tikitin takarar zama shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yayi wa shugaba Buhari wankin babban bargo a garin Abakalki, babban birnin jihar Ebonyi dake a kudu maso gabashin Najeriya.

Atiku Abubakar din dai kamar yadda muka samu ya kamanta gwamnatin shugaba Buhari ne da cewa itace wadda tafi kowace lalacewa musamman ta fannin cin hanci da rashawa tun bayan dawowar demokradiyya a shekarar 1999.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel