Rashawa: Atiku Abubakar yayi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo

Rashawa: Atiku Abubakar yayi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma mai neman tikitin takarar zama shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yayi wa shugaba Buhari wankin babban bargo a garin Abakalki, babban birnin jihar Ebonyi dake a kudu maso gabashin Najeriya.

Atiku Abubakar din dai kamar yadda muka samu ya kamanta gwamnatin shugaba Buhari ne da cewa itace wadda tafi kowace lalacewa musamman ta fannin cin hanci da rashawa tun bayan dawowar demokradiyya a shekarar 1999.

Rashawa: Atiku Abubakar yayi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo

Rashawa: Atiku Abubakar yayi wa Shugaba Buhari wankin babban bargo

KU KARANTA: Saudiyya ta hana wata kasa zuwa hajji da Umara

Legit.ng ta samu cewa Atiku dai ya bayyana hakan ne a lokacin da yake yiwa magoya bayan sa jawabi a babban birnin na Abakalki lokacin da yaje ziyara.

A wani labarin kuma, Babban kamfanin nan na fasahar kere-kere daga kasar China da ke aikin shimfida titin jirgin kasan zamani na cikin garin Abuja watau China Civil Engineering Construction Corporation ya ce har yanzu gwamnatin tarayya bata biya su kudin aikin su ba.

Mahukuntan kamfanin dai sun bayyana cewa aikin na su da suke yi tun a shekarar 2007, yana shan matsala daga bangaren gwamnati domin kuwa har yanzu ba'a biya su kudin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel