'Yan sanda sun damke wani malamin addinin da ya bankado asirrin gwamna a Najeriya

'Yan sanda sun damke wani malamin addinin da ya bankado asirrin gwamna a Najeriya

Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya shiyyar jihar Imo dake a kudu maso gabashin Najeriya sun cafke wani babban malamin addini a jihar mai suna Chukwuma Okezuo bisa zargin sa da laifin yiwa gwamnan jihar Rochas Okorocha kazafi.

Kamar dai yadda muka samu, 'yan sandan sun ce faston a yayin gabatar da wa'azi a majami'ar sa, ya zargi gwamnan da taimakawa bata gari a jihar wajen sace 'yan yara kasa da shekaru 10 da nufin yin tsafi da su a zaben 2019 mai zuwa.

'Yan sanda sun damke wani malamin addinin da ya bankado asirrin gwamna a Najeriya

'Yan sanda sun damke wani malamin addinin da ya bankado asirrin gwamna a Najeriya

KU KARANTA: Dubun yan madigo ta cika a Kano

Legit.ng ta samu cewa wannan ne dai ya sa jami'an 'yan sandan suka yanke shawarar cafke shi domin yayi masu karin bayani game da kalaman nasa da suka ce za su iya tunzura jama'ar jihar.

A wani labarin kuma, Wata babbar kotun tarayya dake zaman ta a garin Minna, babban birnin jihar Neja dake a Arewa ta tsakiyar Najeriya ta bayar da umurnin kwace makudan kudaden da suka kai Naira miliyan 57 da kadarorin da suka hada da gidajen alfarma da motoci na tsohon gwamnan jihar, Mu'azu Babangida Aliyu.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, ranar Talatar da ta gabata ne dai kotun ta bayar da umurnin kwace dukiyar ta tsohon gwamnan sakamakon karar da hukumar EFCC ta shigar a gaban ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel