FAAC: Ana ta rikici tsakanin Kamfanin NNPC da Gwamnatin Tarayya

FAAC: Ana ta rikici tsakanin Kamfanin NNPC da Gwamnatin Tarayya

Labari ya zo mana cewa a jiya ma dai haka nan aka kuma tashi baram-baram wajen taron FAAC kasafta kudin Najeriya na Watan Yuni da ya gabata. Yanzu an dage zaman daga jiya zuwa gobe.

Ana sa rai cewa za a zauna Ranar Alhamis bayan da taron FAAC na watan jiya ya gaza kai ko ina bayan an yi fiye da sa’a guda ana kokarin tattaunawa. Abin dai ya faru ne bayan da NNPC ta gaza zuba wasu kudin kirki a asusun Gwamnati.

FAAC: Ana ta rikici tsakanin Kamfanin NNPC da Gwamnatin Tarayya

Ministar kudi ta nemi NNPC ta zuba kudin da su ka dace a asusun Gwamnati

Jim kadan bayan an fara taron ne Akanta Janar na kasar Ahmed Idris da mukarraban sa su ka fice daga Ma’aikatar kudi inda ake zaman. Barin wajen taron da babban Akanta kasar yayi ya nuna cewa dai akwai babbar matsala har yanzu.

KU KARANTA: Hotunan yadda aka kwashe wajen Kamfen din Ekiti

The Nation ta rahoto cewa Gwamnonin Jihohin kasar sun nuna cewa ba za su amince da kudin da NNPC ta kawo ba. Gwamnonin sun nemi Kamfanin mai na kasar NNPC ta ba Gwamnati cikakken abin da ya dace ta bada na watan da ya wuce.

Idan har aka yi sake dai ba mamaki a kara shiga wani sabon mako babu albashi a Najeriya. Hakan na zuwa ne bayan an gaza shawo karshen sabanin da ke tsakanin NNPC da Gwamnati. Gobe ne za a sake wani zaman a babban Birnin Tarayya Abuja.

Ku na sane cewa a duk karshen wata a kan hadu a Birnin Tarayya Abuja domin ganin yadda za a warewa Jihohi 36 na Kasar da kuma Kananan Hukumomi da Gwamnatin Tarayya kason su. A watan jiya dai ana zargin Hukumar NNPC ta yi coge.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel