Yanzu Yanzu: Za’a rufe gadar Third Mainland domin gyare-gyare

Yanzu Yanzu: Za’a rufe gadar Third Mainland domin gyare-gyare

Babban kwanturola na ayyukan tarrayya dake Lagas, Mista Adedamola Kuti, ya bayyana a ranar Talata, 10 ga watan Yuli cewa an fara tattaunawa kan rufe gadar Third Mailand doming yare-gyare.

Kuti ya bayyanawa kamfanin dillancin labaran Najeriya cewa ma’aikatar ayyuka zata yi wata ganawa tare da masu ruwa da tsaki a ranar Laraba domin tattauna yadda za’a tafiyar da cunkoso a lokacin gyare-gyaren.

Sai dai bai bayyana ainahin ranar da za’a rufe gadar ba ko kuma tsawon lokacin da ayyukan gyare-gyaren zai dauka.

KU KARANTA KUMA: Allah ya rigada ya kadarta cewa Buhari zai fadi a zaben 2019 - Galadima

A cewarsa, masu ruwa da tsakin da za su halarci ganawar domin tattauna gyare-gyaren sun hada da hukumomin kula da cunkoson hanyoyi, mammalakan manyan motoci, kungiyoyin direbobi, da kuma hukumomin tsaro da sauransu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel