'Yan adawa na bata suna na da rikicin makiyaya da manoma

'Yan adawa na bata suna na da rikicin makiyaya da manoma

A yau Talata shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranci tawagar kusoshin jam'iyyar APC zuwa Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti don yin kamfen na karshe ga dan takarar gwamna karkashin APC, Dr. Kayode Fayemi gabanin zaben da za'a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira da mutanen jihar Ekiti su jefa wa Mr. Fayemi kuri'arsu a ranar Asabar saboda su tabbatar da cewa sun kyautata makomar jiharsu da samun cigaba mai dorewa.

A jawabin da ya yi lokacin da yake ganawa da dandazon magoya bayan jam'iyyar APC a Ekiti, ya gargadi masu jefa kuri'ar suyi hankali da karairayi da bita da kulli da yan adawa ke masa game da rikicin makiyaya da manoma a wasu sassan kasar.

Abokan hammaya na min bita da kulli da rikicin makiyaya da manoma - Buhari

Abokan hammaya na min bita da kulli da rikicin makiyaya da manoma - Buhari

DUBA WANNAN: Tabarbarewan Tsaro: Shugabanin kudu da yankin Arewa ta tsakiya sun gana da T.Y Danjuma

Daruruwan mutane sun rasu sakamakon rikicin duk da cewa akwai jami'an tsaro a jihohin. Wasu daga cikin jihohin da rikicin yafi shafa sune Filato da Benue da Taraba.

"Sai dai suna min sharri suna cewa ban dauki mataki game da rikicin makiyaya da manoman ba saboda wai ni bafulatani ne," inji shugaban kasar.

"Sai dai wannan sharri ne kawai. Muna iya kokarin mu wajen ganin mun dakatar da kashe-kashen kuma mu nemo hanyar magance matsalar da dun-dun-dun."

Shugaba Buhari yana mayar da martani ne game da kalaman jam'iyyar PDP a lokacin yakin neman zabensu inda su kayi ikirarin cewa gwamnatin APC bata dauka mataki don kawo karshen rikicin.

Jihar Ekiti na daya daga cikin jihohin da suka kafa dokar hana kiwo a Najeriya kuma wasu jihohin su kayi koyi da ita duk da cewa gwamnatin tarayya ta soki dokar.

Gwamna Ayo Fayose na jihar Ekiti yana daya daga cikin yan adawa dake zargin shugaba Buhari ta yin sakwa-sakwa game da batun kashe-kashen saboda shi bafulatani ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel