Kada kuyi asaran kuri’unku, ku zabi Fayemi – Buhari ga mutanen Ekiti

Kada kuyi asaran kuri’unku, ku zabi Fayemi – Buhari ga mutanen Ekiti

A ranar Talata, 10 ga watan Yuli, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci mutanen Ekiti dkada su yi asaran kuri’unsu a zaben gwamna da za’a yi a ranar Asabar.

Maimakon haka, shugaban kasar ya bukaci masu zabe da su zabi dan takarar jam’iyyar All Progressives Party (APC), Dr Kayode Fayemi, tare da nuni ga kokarin jam’iyyar mai mulki a kasar.

Buhari wanda ya bayyana hakan a gangamin karshe na jam’iyyar a Ado-Ekiti, ya fadama magoya bayan jam’iyyar da suka taru a filin asa na Oluyemi Kayode Stadium cewa babu wani dan takara da fi Fayemi.

Ya ce kada mutane Ekiti su bari a yaudare su da shirin ciyarwa na gwamnatin PDP a jihar, ya bayyana hakan a matsayn abun da akan yi domin durkushe dimokradiyya.

Kada kuyi asaran kuri’unku, ku zabi Fayemi – Buhari ga mutanen Ekiti

Kada kuyi asaran kuri’unku, ku zabi Fayemi – Buhari ga mutanen Ekiti

Ya bukaci al’umman jihar da su duba tarin ayyukan da gwamnatin tarayya ke yi a fadin jihar domin inganta rayukan talakawanta.

KU KARANTA KUMA: Allah ya rigada ya kadarta cewa Buhari zai fadi a zaben 2019 - Galadima

A halin da ake ciki, Mallam Bolaji Abdullahi, babban sakataren labarai na jam’iyyar All Progressives Congress yace kungiyar sabuwar APC (R-APC) ba kungiyar adawar jam’iyya mai mulki ba ce ya kara da cewa har yanzu APC na nan a hade karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Abdullahi yace kungiyar R-APC sun yi maja da jam’iyyun adawa gabannin zaben 2019.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel