‘Yan sanda sun haramta duk wani taron jama’a gabanin gurfanar da El-Zakzaky gobe

‘Yan sanda sun haramta duk wani taron jama’a gabanin gurfanar da El-Zakzaky gobe

Hukumar ‘yan sanda reshen jihar Kaduna ta sanar da haramta duk wani nau’in taron jama’a gabanin gurfanar da shugaban kungiyar mabiya shi’a na Najeriya, Ibrahim El-Zakzaky, a gobe Laraba.

A wani jawabi da hukumar ta fitar ta ofishin kakakinta, Mukhtar Aliyu, a yau, Talata, ta bayyana cewar zata zuba jami’anta a kowanne lungu da sako na garin Kaduna.

Y ace magidanta su saka idanu sosai a kan unguwannin da suke tare da bukatarsu das u sanar da hukuma duk wani motsin jama’a da basu amince da shi ba.

‘Yan sanda sun haramta duk wani taron jama’a gabanin gurfanar da El-Zakzaky gobe

El-Zakzaky

Muna sanar da mutanen garin Kaduna masu biyayya ga doka da kada su tayar da hankalinsu domin zamu tabbatar da ba a samu barkewar wani tashin hankali ko rikici ba,” a cewar Aliyu.

Aliyu ya jaddada cewar yin kowanne irin nau’in taro bai halasta ba tare da sanar da cewar kuma hukumar ‘yan sanda zata gauraya ga duk wanda ya saba doka da oda.

DUBA WANNAN: Kiyayewar Allah: dakarun soji sun kashe wutar wani rikicin kabilanci da ya so barkewa a jihar Gombe

Ya kara da cewar daga cikin matakan da hukumar ‘yan sanda zata dauka domin ganin ba a samu sabawa doka ba, akwai rufe wasu manyan hanyoyi a cikin garin Kaduna da suka hada da Titin Independence, Bida Road da kuma duk hanyoyin da zasu sada mutum da tititn Ibrahim Taiwo.

‘Hukumar ‘yan sanda na kira ga jama’a da su sanar da ita al’amuran dukkan mutanen da basu amince da su ba a yankin da suke zaune ko gudanar da sana’o’i

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel