Bana tunanin sabuwar jam’iyyar da PDP ta kafa zata iya tunkudar da jam’iyya mai mulki – Balarabe Musa

Bana tunanin sabuwar jam’iyyar da PDP ta kafa zata iya tunkudar da jam’iyya mai mulki – Balarabe Musa

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa, yace kulla yarjejeniya da jam’iyyu da kungiyoyin siyasa 39 suka yi gabannin zaben 2019 ba komai bane face “kaguwa”.

Musa ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai a ranar Talata, 10 ga watan Yuli a Abuja.

Ya ce: “Bana tunanin sabuwar jam’iyya irin wannan dake cike da wadanda suka kagu zata iya kayar da jam’iyya mai mulki, wato APC.”

Idan baza ku manta ba Legit.ng ta ruwaito cewa jam’iyyun Peoples Democratic Party (PDP), Social Democratic Party (SDP) da wasu kungiyoyi da jam’iyyun siyasa 37 sun kulla yarjejeniya a ranar Litinin, 10 ga watan Yuli akan zaben 2019.

Shugabannin jam’iyyun sun sanya hannu a yarjejeniyar inda suka yi alkawarin aiki tare karkashin Coalition for United Democratic Parties (CUDP) domin fitar da dan takara guda a zabe mai zuwa.

Bana tunanin sabuwar jam’iyyar da PDP ta kafa zata iya tunkudar da jam’iyya mai mulki – Balarabe Musa

Bana tunanin sabuwar jam’iyyar da PDP ta kafa zata iya tunkudar da jam’iyya mai mulki – Balarabe Musa

Musa wadda ya kasance shugaban jam’iyyar , Peoples Redemption Party (PRP) ya nisanta jam’iyyarsa daga wannan sabuwar jam’iyya.

KU KARANTA KUMA: Allah ya rigada ya kadarta cewa Buhari zai fadi a zaben 2019 - Galadima

A cewarsa abun da ake bukata shine wata jam’iyya da tunaninta ya fi na APC amma ba wai kawai wani ra’ayi da ya sha bambam da na APC ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel