Tsoron kungiyar kwadago ya saka MTN rufe ofishinta na Abuja

Tsoron kungiyar kwadago ya saka MTN rufe ofishinta na Abuja

Kamfanin sadarwa na MTN ta rufe hedkwatanta dake Maitama a Abuja sakamakon zanga-zanga da hukumar kwadago na kasa NLC keyi game da yadda kamfanin ke saba wasu dokokin kungiyar.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa ofishin a safiyar yau Talata ofishin na kulle kuma babu kowane ma'aikata sai dai 'dan sanda da wani mai gadi a kofar shiga.

NAN ta ruwaito cewa kungiyar kwadagon ta fara gudanar da zanga-zangar a ofisoshin MTN ne tun ranar Litinin a wasu jihohin Najeriya saboda rashin dakile hakkin ma'aikata da kamfanin keyi.

Kamfanin sadarwa na MTN ta kulle ofishin ta dake Abuja

Kamfanin sadarwa na MTN ta kulle ofishin ta dake Abuja

DUBA WANNAN: Hukumar Kwastam ta kama manyan bindigogi sama da 200,000 a jihar Neja

Shugabanin kungiyar kwadagon tare da mambobinsu sun gudanar da wata zanga-zanga a babban hedkwatan MTN dake Legas a ranar Litinin inda suka hana shige da fice na misalin sa'o'i takwas wanda hakan ya kawo tangardar aiki a ranar.

Wani mai gadin kamfanin da ya nemi a sakayya sunansa ya shaidawa NAN a Abuja cewa an bayar da umurnin daga hedkwatan kamfanin dake Legas cewa dukkan ma'aikatan su zauna a gidajensu har sai lokacin da ake nemi su.

"Wata kila saboda zanga-zangar da wasu mutane su kayi a ofishin mu ne Legas ne ya janyo hakan.

"An bawa dukkan ma'aikata umurnin suyi zamansu a gidajensu har sai lokacin da aka nemi su, inji shi.

Mai gadin ya kara da cewa akwai alamun idan matsi ya yi yawa, kamfanin na iya tattara komatsansu su bar Najeriya saboda irin takunkumin kasuwanci da ake kafa musu a kasar.

An gudanar da irin wannan zanga-zangar a ofisoshin kamfanin dake Fatakwal, Yenagoa, Kano, Ibadan da wasu garuruwan a ranar Litinin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel