Kafa hadakar jam’iyyu ta CUPP ba zai hana Buhari cin zaben 2019 - APC

Kafa hadakar jam’iyyu ta CUPP ba zai hana Buhari cin zaben 2019 - APC

- Bayan kafa wata babbar rundunar hadawa a jiya wadda ta kunshi jam'iyyu 39 karkashin PDP, jam'iyyar APC ta ce bata tsorata ba

- Kafa rundunar hadakar ma dai zai kara mata karfin gwiwa ne ta sake shiri kafin zabe mai zuwa

Sakataren jam’iyyar APC a jihar Nassarawa Alhaji Aliyu Bello, ya ce sabuwar hadakar da PDP ta kafa mai take CUPP ba za ta iya dakatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zarcewa idan anzo zaben 2019.

Kafa hadakar jam’iyyu ta CUPP ba zai hana Buhari cin zaben 2019 - APC

Kafa hadakar jam’iyyu ta CUPP ba zai hana Buhari cin zaben 2019 - APC

Bello ya shaida hakan ne ga manema labarai a yau Talata, inda ya ce mutane ne suka zabi shugaba Buhari a zaben 2015 kuma har yanzu suna sonsa zasu sake zabarsa.

Ya kara da cewa waccan hadakar ba ta koma face ta ‘yan siyasa wadanda ransu bai so irin cigaban da Buhari ya samar ba a Najeriya ba, musamman bangaren yaki da cin hanci da rashawa.

KU KARANTA: Hadakarmu da PDP ba maja ce ba – Shugaban jam’iyyar APP

Kashi 90% na ‘yan Najeriya masu jefa kuri’a ne ba mambobin jam’iyya ba, kuma su ne shugaban kasa ke saran zasu zabe sa. Kowa shaida ne kan yadda mutane kan fito tarbarsa a duk sanda ya je wani wuri ziyara. Bello ya jaddada.

Kafa hadakar jam’iyyu ta CUPP ba zai hana Buhari cin zaben 2019 - APC

Kafa hadakar jam’iyyu ta CUPP ba zai hana Buhari cin zaben 2019 - APC

Kowacce jam’iyya tabbas bata son asarar koda mutum daya daga cikin ‘ya’yanta, sai dai APC zata dauki waccan hadaka a matsayin wani yunkuri da zai zaburar da ita gabannin zaben 2019.

“Kamar yadda muke wasu suke barinmu haka muma zamu shawo kan wasu su shigo mu cikinmu” ya shaida

Daga karshe Bello ya bayyana amannar da suke da ita a kan hukumar zabe ta kasa (INEC) don ganin ta gudanar da sahihin zabe gamsasshe a 2019.

Babbar jam’iyyar adawa ta kasa PDP ta shawo kan wasu jam’iyyu 30 suka kafa wata hadaka da sukaiwa lakabi da CUPP ciki har da wani tsagi na jam’iyyar APC mai suna rAPC karkashin Buba Galadima.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel