Rashin sanin yawan mutanen dake dauke da cutar kanjamau na kawo mana cikas – Buhari

Rashin sanin yawan mutanen dake dauke da cutar kanjamau na kawo mana cikas – Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa rashin sanin ainahin yawan mutanen dake dauke da cuta mai karya garkuwar jikin dan adam wato kanjamau a kasar na da cikin kalubalan dake hana Najeriya samun tallafin magungunan cutar daga kasashen waje.

Shugaban kasar ya sanar da hakan ne a fadar gwamnati a yayin kaddamar da taron fara kididdiga na yawan mutanen da ke dauke da cutar kanjamau a kasar.

Buhari ya ce domin kawar da irin wadannan matsalolin ne gwamnati ta amince kan yin kidaya domin samun adadin yawan mutanen dake dauke da cutar.

Rashin sanin yawan mutanen dake dauke da cutar kanjamau na kawo mana cikas – Buhari

Rashin sanin yawan mutanen dake dauke da cutar kanjamau na kawo mana cikas – Buhari

Buhari ya ce kidayan zai dauki tsawon watanni shida a duka fadin kasar nan.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Alhaji Buba Galadima, shugaban kungiyar sabuwar APC (R-APC) ya shawarci shugaban kasa Buhari da ajiye kudirinsa na sake takara a 2019 saboda zai sha kashi.

KU KARANTA KUMA: Tambuwal ya daura alhakkin kashe-kashe akan gazawar shugabanci

Galadima, wadda kungiyarsa ta R-APC ta hade da sauran jam’iyyun siyasa a ranar Litinin, 9 ga watan Yuli, yace Allah ya kaddata cewa shugaba Buhari zai fadi a zaben 2019.

Ya kuma yi zargin cewa mambobin kungiyar siyasar sa na fuskantar barzanar mutuwa tunda suka bar APC ta hanyar sakonni.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel