2019: Idan Shugaba Buhari ya koma mulki akwai matsala Inji Matasan Arewa

2019: Idan Shugaba Buhari ya koma mulki akwai matsala Inji Matasan Arewa

Mun samu labari jiya cewa wasu Matasan da ke Yankin Arewacin Najeriya sun bayyana cewa akwai babbar matsala idar har Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zarce da mulkin kasar nan don haka ya ba wadanda su ka cancanta su cigaba.

A jiya Litinin Kungiyar nan ta AYCF ta Matasan Arewa tace idan har Shugaba Buhari ya cigaba da mulki bayan 2019 to lallai Arewa da sauran bangarorin kasar nan sun shiga uku sun lalace ganin irin abubuwan da ke faruwa a yanzu a kasar.

Kungiyar ta AYCF ta maida martani ne ga ‘Yan Majalisun Yankin Arewa da su ka yi wa Shugaban kasa Buhari mubaya’a a Garin Kaduna a makon can. Matasan Yankin sun ce abin da ya dace shi ne Buhari ya tafi ya ba wani ‘Dan Arewa dama.

KU KARANTA: Ministan mai ya bayyana irin gaskiyar Buhari

‘Yan Majalisar Tarayya daga Jihohin Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Jigawa, Sokoto da Zamfara sun nuna cewa su na bayan Shugaban kasa Buhari a 2019 domin karasa irin manyan ayyukan gina kasa da inganta tsaro da ya faro a Najeriya.

Sai dai Matasan da ke karkashin lemar AYCF sun ce kashe-kashen da ake yi a kasar nan ya isa haka kuma ko sauro ba a damke ba don haka su ka nemi Shugaba Buhari ya ba wani ‘Dan siyasa dama a zaben 2019 domin kasar ta zauna kalau.

Shugaba Buhari dai yace ya san wadanda su ke da hannu a wannan kashe-kashe da ake yi, sai dai har yanzu ba a kama su ba. Don haka ne Shugaban Kungiyar Matasan Gambo Gujungu ya ke ganin da gan-gan Gwamnati ta bari ake kashe mutane.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel