Shiru ka ke ji: Ministar kudi ta gaza cewa uffan a kan batun badakalar satifiket

Shiru ka ke ji: Ministar kudi ta gaza cewa uffan a kan batun badakalar satifiket

Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun ba ta ce komai ba har yanzu bayan an dauki fiye da sa’a 48 da aka zarge ta da amfani da wata shaidar bogi. Ana zargin cewa Ministar na amfani ne da takardar bautar kasa na NYSC na jabu.

Shiru ka ke ji: Minista Adeosun ta gaza cewa uffan a kan batun badakalar satifiket

Ministar kudin Najeriya Kemi Adeosun a bakin aiki

A karshe Hukumar NYSC ta fito tayi magana jiya inda tace za ta binciki zargin da ake yi na cewa Ministar ba tayi wa kasar ta hidima ba. Ana zargin Ministar kasar da tsallake hidimar kasar da ake yin a karya da kuma amfani da takardun bogi.

KU KARANTA: An hurowa Shugaban kasa Buhari wuta ya tsige Ministar Kudi

A jiya ne Hukumar NYSC ta maida martani game da zargin na Jaridar Premium Times inda tace maganar gaskiya Kemi Adeosun ta nemi a ba ta takardar tsallake bautar kasar da ake yi idan har shekarun mutum sun zarce 30 a Duniya.

Wata Jami’ar Hukumar mai suna Adenike Adeyemi tace NYSC za ta binciki lamarin ko da cewa babu tabbacin cewa an ba Adeosun takardar da ta bukata a lokacin. Ita dai Ministar har yanzu ba tace komai ba game da lamarin duk da wannan abu.

‘Yan Jarida sun yi kokarin tuntubar Oluyinka Akintunde wanda shi ne ke magana da yawun bakin Ministan, shi ma bai ce komai ba. Yanzu dai har wasu manyan Lauyoyi sun fara kira a kori Ministar daga aiki saboda saba dokar kasar da tayi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel