An kama shi yana sayar da aikin bogi

An kama shi yana sayar da aikin bogi

Wata babbar kotu a jihar Gombe ta bada umarnin a garkame wani mutum mai shekaru 42 a gidan kaso, sakamakon yin abu na jabu da kuma saida takardar daukar aiki na karya

An kama shi yana sayar da aikin bogi

An kama shi yana sayar da aikin bogi

Wata babbar kotu a jihar Gombe ta bada umarnin a garkame wani mutum mai shekaru 42 a gidan kaso, sakamakon yin abu na jabu da kuma saida takardar daukar aiki na karya.

Wanda ake zargin mai suna Yusuf Abba wanda yake zaune a Tudun wada cikin kwaryar jihar ta Gombe ana tuhumar sa ne da bada takardar daukar aiki ta bogi ga wasu mutane biyu.

DUBA WANNAN: An kama wanda ya kashe Diyar tsohon mataimakin gwamnan Ondo

A bayanin da kotun ta fitar tace a tsakanin watan Yuni da Yuli na shekarar 2017 wanda ake zargin yaje wata bariki dake karamar hukumar Deba ta Yalmatu ya karbi kudi N140,000 daga hannun Kwatiri Bandita sannan ya bata takardar shaidar daukar aiki ta bogi a Polytechnic dake garin Bajoga.

Kotun ta kara da cewa wanda ake zargin ya kara karbar kudi N120,000 daga hannun Janeth Ali wanda ke garin Nayi Nawa a cikin jihar Gombe.

Jami'in dan sanda Inspector Bako Shekari ya bayyana wa kotu cewa wannan laifi ya sabawa doka ta 320 sannan wanda ake zargin ya amsa laifin sa a yayin da ake tuhumar sa.

Saboda haka ne alkalin kotun Mai sharia Daurabo Sulaiman Sikam ya bada umarnin a garkame shi a gidan kaso sannan kuma ya dage sauraron karar zuwa 19 ga watan Yulin wannan shekarar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel