Rikicin APC: Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya ya nemi Nyako da Ribadu su yi zaman su a Jam’iyya

Rikicin APC: Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya ya nemi Nyako da Ribadu su yi zaman su a Jam’iyya

Mun ji labari daga Jaridar Daily Trust cewa Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya watau Babachir David Lawal ya nemi Murtala Nyako da irin su Nihu Ribadu su zauna a Jam’iyyar APC mai mulki.

Injiniya Babachir David Lawal ya zauna da ‘Yan R-APC wadanda kafar su daya ta bar Jam’iyyar APC inda ya nemi su yi hakura su zauna a Jam’iyyar. Babachir ya gana ne da Magoya bayan tsohon Gwamna Murtala Nyako.

Rikicin APC: Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya ya nemi Nyako da Ribadu su yi zaman su a Jam’iyya

Ana neman Magoya bayan Nyako su hakura su zauna a APC

Kamar yadda mu ka samu labari har da Magoya bayan tsohon ‘Dan takarar Gwamnan Adamawa Nuhu Ribadu aka yi wannan zama. Injiniya David Lawal ya nemi ‘Yan siyasan na Jihar Adamawa su yi watsi da tafiyar R-APC.

KU KARANTA: Ko babu 'Yan rAPC za mu kai labari - APC

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya bayyana cewa ‘Yan rAPC din ba kowan kowa bane su kuma ba za su kai labari ba. David Lawal yace Shugaban Bangaren na rAPC Buba Galadima bai isa yayi wa APC wani abu ba.

Tsohon SGF din na Gwamnatin Buhari yace su Buba Galadima ba su ji dadin kafa Jam’iyyar APC tun farko ba kuma wannan ne ya sa Shugaban kasa Buhari yayi watsi da su kuma ya ci zabe a 2015 ba tare da gudumuwar su ba.

A karshen zaman da aka yi Magoya bayan Gwamna Murtala Nyako sun ce su na nan a Jam’iyyar APC amma ba za su yadda a ba Gwamna Muhammadu Jibrilla Bindow tikitin tazarce a sama ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel