Hukumar soji ta saki kananan yara da Boko Haram ke amfani da su wajen yaki

Hukumar soji ta saki kananan yara da Boko Haram ke amfani da su wajen yaki

Hukumar sojin Najeriya ta mika wa gwamnatin jihar Borno da majalisar dinkin duniya (UN) yara guda 183 da aka samu suna yiwa Boko Haram hidima domin a basu taimakon da ya dace kafin a sada su da iyalansu.

A jawabinsa wajen taron mika yaran da akayi a jiya a Maiduguri, Shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya, Laftanat Janar Tukur Buratai ya ce yaran da aka saki sun hada da mata takwas da maza guda 175.

Buratai wanda ya samu wakilcin kwamandan Opertion Lafiya Dole, Manjo Janar Rogers Nicolas ya ce yaran na bukatar kulawa na musamman da kuma horo.

Soji sun saki almajiran da Boko Haram ke koyawa yaki

Soji sun saki almajiran da Boko Haram ke koyawa yaki

KU KARANTA: Martanin shugaba Buhari kan hukuncin da kotu ta yanke kan Bukola Saraki

"Za'a saki dukkan yaran da aka kama kuma aka yi musu tambayoyi, zamu mika yara 183 da muka samu da hannu cikin ta'addancin Boko Haram ga gwamnatin jihar Borno da Majalisar Dinkin Duniya kamar yadda ka'idar aiki ya tanada," inji shi.

A bangarensa, gwamnan jihar Borno Kashim Shettima wanda ya samu wakilcin kwamishinan harkokin mata, Hajiya Fanta Babashehu, ya mika godiyarsa ga shugaban hafsin sojin kasan saboda sakin yaran da ya yi.

Wakilin UN a taron, Ibrahim Sesay, ya ce tun shekarar 2017, Asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta bayar da tallafi ga yara sama da 8,700 da aka karbo daga kungiyoyin ta'addanci.

Mr Sesay ya ce, zamu cigaba da aiki da gwamnatin jihar Borno da ma'aikatar harkokin mata da cigaban al'umma da sauran masu ruwa da tsaki don ganin an koyar da yaran sana'o'i da kuma dukkan taimakon da suke bukata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel