Gwamnan Ekiti Fayose na kokarin hana Shugaban kasa Buhari zuwa kamfe

Gwamnan Ekiti Fayose na kokarin hana Shugaban kasa Buhari zuwa kamfe

Mun samu labari daga wani babban ‘Dan Jam’iyyar APC kuma a Jihar Ekiti kuma mai ba Shugaban kasa shawara watau Babafemi Ojudu cewa Gwamnan Jihar Mai Girma Ayo Fayose na kokarin hana Shugaba Buhari shiga Ekiti.

Gwamnan Ekiti Fayose na kokarin hana Shugaban kasa Buhari zuwa kamfe

Mai ba Shugaban kasa Buhari shawara Ojudu yace Fayose ya shirya tsiya

Babafemi Ojudu yayi bayani a shafin sa na Facebook cewa Gwamna Ayodele Peter Fayose na neman hana motoci yawo a Jihar ne domin ganin Shugaban Kasa Buhari bai samu shigowa Jihar ba kamar yadda ya tsara.

A yau Talata 10 ga Wata ne dai aka shirya cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai zo Garin Ekiti domin yi wa ‘Dan Takarar Jam’iyyar APC kuma Ministan sa Kayode Fayemi kamfe na zaben da za ayi kwanan nan.

KU KARANTA:

Ojudu ya bayyana cewa Gwamna Fayose ya biya masu motocin haya kudi su zauna a gida domin ganin Magoya bayan Jam'iyyar APC sun rasa abin hawa. Ojudu yake cewa yanzu haka duk an ajiye motocin haya a Gidan Gwamna an rufe su.

Bayan nan ma dai Gwamna Fayose ya sa an rufe kasuwanni ya kuma hana kowa ya fito ya tarbi Shugaban kasa Buhari. Sai dai duk da haka Ojudu yace sun shirya wata dabarar tsaf domin ganin Shugaba Buhari bai ji kunya ba.

Dazu kun ji cewa Kayode Fayemi wanda ya fito takarar Gwamnan Jihar Ekiti yana cigaba da kamfe. Fayemi wanda tsohon Gwamnan Ekiti ne ya rabawa al’umma fetur kyauta jiya a babur. Fayose dai rikakken 'Dan adawan Shugaba Buhari ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel