IG da INEC sun gaza shawo kan hargitsi tsakanin APC da PDP yayin taron masu ruwa da tsaki a Ekiti

IG da INEC sun gaza shawo kan hargitsi tsakanin APC da PDP yayin taron masu ruwa da tsaki a Ekiti

Taron masu ruwa da tsaki a zaben gwamnan jihar Ekiti da za a yi ranar 14 ga watan Yuli ya tashi ba shiri bayan barkewar cece-kuce tsakanin magoya bayan jam'iyyar APC da na PDP.

A wurin taron masu ruwa da tsakin akwai shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmoud Yakubu, shugaban rundunar 'yan sanda na kasa, Mista Ibrahim Idris, 'yan takara da shugabannin jam'iyyu daban-daban, sarakunan gargajiya, shugabannin hukumomin tsaron da sauransu.

IG da INEC sun gaza shawo kan hargitsi tsakanin APC da PDP yayin taron masu ruwa da tsaki a Ekiti

IG da INEC sun gaza shawo kan hargitsi tsakanin APC da PDP yayin taron masu ruwa da tsaki a Ekiti

KU KARANTA: Martanin shugaba Buhari kan hukuncin da kotu ta yanke kan Bukola Saraki

Yayin tattaunawa a wurin taron, wakilin jam'iyyar PDP ya bayyana damuwarsa bisa tabbatar da tsaro yayin zaben tare da yin zargin cewar jam'iyyar APC na amfani da jami'an tsaro domin cin zarafin 'yan jam'iyyar su. Jim kadan bayan kammala jawabinsa ne sai magoya bayan PDP dake da yawa a wurin suka fara ihu ba kakkautawa.

Magoya bayan na PDP sun cigaba da yin ihun bayan wakilin jam'iyyar APC ya yi kokarin tankawa wakilin jam'iyyar su.

Duk kokarin IG, da shugaban hukumar INEC da shugaban majalisar sarakuna na jihar, Oba Michael Ademolaju, ta shawo kan hayaniyar da ta barke ya ci tura.

Da yake magana a wurin taron, shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmoud, ya bayar da tabbacin cewar hukumar sa zata gudanar da sahihin zabe.

Kazalika, a nasa bangaren, shugaban rundunar 'yan sanda ta kasa, Ibrahim Idris, ya yi alkawarin tabbatar da tsaro yayin zaben da za a yi ranar Asabar, 14 ga watan Yuli, mai zuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel