Gwamna Ortom na shirin barin APC

Gwamna Ortom na shirin barin APC

Duk yunkuri da gwamnonin jam’iyya mai mulki na ganin sun sasanta Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue da shugaban kasa Muhammadu Buharibai yiwu ba, inda hakan ya sa jihar ta shiga tsaka mai wuya ta fannin siyasa yayinda gwamnan ke yunkurin ficewa daga jam’iyya mai mulki.

Shirin ficewar gwamnan ya kara kamari ne a karshen makon lokacin da ya soke majalisar jihar sannan ya dakatar da hadiman na hannun damansa a harkar siyasa, Sanata George Akume.

A yayin da gwamnan ya soke majalisar, sai ya dawo nda kwamishinoni hudu, wadanda kowa ya san basu da kowani alaka da Akume, tsohon gwamnan jihar wanda ya taka rawar gani a harkar siyasar jihar.

Yiwuwar ficewar Ortom daga APC ya samo asali ne ta fuskacin ganin gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyarsa ta kasa magance hare-haren da makiyaya ke kaiwa mutane a jiharsa.

A wani yunkuri da suke don ganin sun hana shi sauya shekar, kungiyar gwamnonin APC, sun kafa wata kwamiti watanni biyu da suka shige domin gyara alaka tsakanin gwamnan da shugaban kasa.

Gwamna Ortom na shirin barin APC

Gwamna Ortom na shirin barin APC

Gwamna Kashim Shettima na jihar Borno ne ke jagorantar kwamitin sannan a ciki akwai gwamnonin Kaduna, da Adamawa a matsayin mambobi.

KU KARANTA KUMA: An bukaci gwamnatin Najeriya da ta zakulo masu haddasa kashe-kashe

Ga dukkan alamu wannan yunkuri ya gaza, bayan yunkuri mai ban al’ajabi da gwamnan yayi na soke majalisar a karshen makon da ya gabata.

Majiyoyi sun bayyana cewa da yiwuwar gwamnan zai koma tsohuwar jam’iyyarsa ta PDP.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel