Zaben Ekiti: Fayemi ya shiga yakin neman zaben Gwamna gadan-gadan

Zaben Ekiti: Fayemi ya shiga yakin neman zaben Gwamna gadan-gadan

Mun samu labari cewa jiya Ministan Ma’adanai na Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari watau Dr. Kayode Fayemi wanda ya fito takarar Gwamnan Jihar Ekiti yana cigaba da kamfe.

Kayode Fayemi wanda tsohon Gwamnan Ekiti ne ya shiga yakin neman zaben Gwamnan Jihar gadan-gadan inda yake sa ran komawa kujerar sa. Hakan ta sa ‘Dan takarar na APC ya rabawa ‘Yan acaba man fetur kyauta jiya.

Zaben Ekiti: Fayemi ya shiga yakin neman zaben Gwamna gadan-gadan

Kayode Fayemi ya rabawa 'Yan acaba lita 5 na man fetur

Ministan na kokarin ganin yayi nasara wannan karo ya doke ‘Dan takarar Jam’iyyar PDP wanda a yanzu haka shi ne Mataimakin Gwamna Ayo Fayose. Fayemi dai ya raba fetur ne kyauta a wani gidan mai da ke Ajilosun a Garin Ekiti.

Wadanda ke tare da ‘Dan takarar na APC sun samu lita 5 na mai a kyauta saboda goyon bayan da su ka nuna masa. Ana kuma sa rai yau za a cigaba da rabon man. Haka kuma masu hawa motar haya za su hau ne duk a kyauta a yau dinnan.

KU KARANTA: Za mu yi nasara ko da 'Yan R-APC ko babu su - APC

‘Dan takarar Gwamnan ya fadawa masu motoci ka da su karbi kudin kowa domin kuwa duk zai biya. Fayemi dai duk yana sa rai ne cewa zai koma kujerar da ya bari a 2014 inda ya sha kasa hannun Gwamna mai-ci Ayodele Fayose.

Kamar yadda labari ya zo mana, Kayode Fayemi ya nemi Jama’a su yi watsi da rade-radin da ke yawo na cewa zai hana acaba inda yace sai ma dai ya kawo gyara a harkar kamar yadda yayi lokacin yana Gwamna daga 2010 zuwa 2014.

Kwanaki kun ji cewa Jam’iyyar PDP ta caccaki Shugaban kasa Muhammadu Buhari wajen kamfen din da tayi na neman Gwamnan Jihar Ekiti inda Uche Secondus yace Matasan Najeriya ba Malalata

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel