Wani na-kusa da Jonathan ya gargadi Shugaba Buhari game da ‘Yan R-APC

Wani na-kusa da Jonathan ya gargadi Shugaba Buhari game da ‘Yan R-APC

Mun samu labari cewa wani tsohon ‘Dan Jam’iyyar PDP watau Dr. Doyin Okupe yayi kira ga Jam’iyyar APC tayi kaffa-kaffa da ‘Yan R-APC da ka su ka ja daga da Jam’iyyar ta APC mai mulki.

Wani na-kusa da Jonathan ya gargadi Shugaba Buhari game da ‘Yan R-APC

Shugaban ‘Yan R-APC Injiniya Buba Galaima da 'Dan jarida

Doyin Okupe wana yayi aiki da tsofaffin Shugaban kasar nan Goodluck Jonathan da kuma Olusegun Obasanjo yace ka da APC tayi gigin watsi da su Injiniya Buba Galadima wadanda su ka bangare su ka kafa R-APC.

Okupe yayi wannan bayani ne a gidan Talabijin na Channels inda yake maida martani game da kalaman da wani ‘Dan Jam’iyyar APC Alwan Hassan yayi. Hassan yace idan su Saraki sun ga dama su fice daga Jam’iyyar ta APC.

KU KARANTA: Manyan Jam'iyyu sun shirya tika Buhari da kasa

Tsohon mai ba Jonathan shawara ya bayyana cewa irin kuskuren da Jam’iyyar PDP tayi kenan a 2015 inda Shugaban PDP Bamanga Tukur ya rika cika-baki cewa za su tika APC da kasa ko da babu ‘Yan nPDP sai ga shi PDP ta sha kashi.

A cewar Dr. Doyin Okupe bai dace APC tayi watsi da Bukola Saraki ba don kuwa yana da Jihar Kwara a hannun sa. Okupe ya yabawa irin su Shgaban Majalisar Dattawan Bukola Saraki da Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.

A karshe dai Doyin Okupe da yanzu ya bar PDP ya nemi APC ka da ta bari Shugaba Buhari ya sake takara. Okupe yace idan Buhari yaci zabe akwai matsala kuma idan ya fadi akwai matsala don haka gara kurum ya hakura da tazarce a huta.

Jiya idan ba ku manta ba kun ji cewa PDP ta kira manyan shugabannin ta domin ta zauna game da ‘Yan bangaren R-APC da ba mamaki su ke shirin dawo cikin Jam’iyyar adawar a halin yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel