Hukumar jin dadin mahajjatan Najeriya ta sanar da ranar fara jigilar mahajjata

Hukumar jin dadin mahajjatan Najeriya ta sanar da ranar fara jigilar mahajjata

Hukumar nan dake da alhakin jin dadi da walwalar mahajjatan Najeriya mallakin gwamnatin tarayya watau National Hajj Commission (NAHCOM) a takaice ta saka ranar 21 ga wannan watan na Juli a matsayin ranar fara jigilar mahajjata zuwa kasa mai tsarki.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na hukumar ya fitar wakilin wannan jaridar ya kuma gani.

Hukumar jin dadin mahajjatan Najeriya ta sanar da ranar fara jigilar mahajjata

Hukumar jin dadin mahajjatan Najeriya ta sanar da ranar fara jigilar mahajjata

KU KARANTA: Wasu dalibai a BUK sun fallasa yadda malamai ke lalata da su

Legit.ng ta samu cewa a cikin sanarwar, hukumar ta kuma bayyana ranar 18 ga wannan watan din dai a matsayin ranar rufe karbar kudin zuwa hajjin daga mahajjatan kasar.

A wani labarin kuma, Mahukunta a hukumar rukunin kamfanonin da ke kula da albarkatun man fetur da iskar gas na kasa watau Nigerian National Petroleum Corporation, NNPC a takaice a ranar Litinin din da ta gabata sun sa hannu a wata yar jejeniyar gina matatar iskar gas bakwai.

Kamar yadda muka samu, idan aka kammala matatun iskan gas din, za su rika samar da iskan da ya kai ma'aunin iskar biliyan 3.5 a kullum wanda kuma ana sa ran kammala hakan ne zuwa shekarar 2020.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel