Canji: Gwamnatin Buhari za ta soma gina sabbin matatun iskar gas 7

Canji: Gwamnatin Buhari za ta soma gina sabbin matatun iskar gas 7

Mahukunta a hukumar rukunin kamfanonin da ke kula da albarkatun man fetur da iskar gas na kasa watau Nigerian National Petroleum Corporation, NNPC a takaice a ranar Litinin din da ta gabata sun sa hannu a wata yar jejeniyar gina matatar iskar gas bakwai.

Kamar yadda muka samu, idan aka kammala matatun iskan gas din, za su rika samar da iskan da ya kai ma'aunin iskar biliyan 3.5 a kullum wanda kuma ana sa ran kammala hakan ne zuwa shekarar 2020.

Canji: Gwamnatin Buhari za ta soma gina sabbin matatun iskar gas 7

Canji: Gwamnatin Buhari za ta soma gina sabbin matatun iskar gas 7

KU KARANTA: Tinubu ya tona babban asirin yan PDP

Legit.ng ta samu cewa da yake tsokaci jim kadan bayan sanya hannu a takardar yarjejeniyar, shugaban rukunin kamfanin, Mista Mai Kanti Baru ya bayyana cewa hakan ya zama dole ne idan dai har ana son samun cigaba mai dorewa a kasar nan.

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta gyaran da'a da tabbatar da tarbiyya ta jihar Kano a karkashin jagorancin babban malamin nan na addini, Sheikh Malam Aminu Daurawa ta sha alwashin kaddamar da binciken kwakwaf don gano ainihin gaskiyar faifan sautin wasu 'yan madigo da ya watsu a kafar sadarwar zamani a jihar.

Majiyar mu dai ta Daily Nigerian ra ruwaito cewa faifan sautin dauke da munanan kalaman batsa na wasu 'yan mata ne dai aka yi ta yamadidi da shi musamman ma kafafen sadarwar zamani a ciki da wajen jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel