Hadakarmu da PDP ba maja ce ba – Shugaban jam’iyyar APP

Hadakarmu da PDP ba maja ce ba – Shugaban jam’iyyar APP

- Zaben 2019 na kara karatowa yanayin siyasa na kara dumama

- Jam'iyyar PDP ta jagoranci wasu jam'iyyu da yawa duk don ganin sun kada APC

- Guda daga cikin shuwagabannin jam'iyyun ne da suka yi waccan hadaka ya tabbatar da kasacewarsu cikin shiri na kome zai faru sun shirya masa

Shugaban jam’iyyar Action Peoples Party (APP) Mr Ikenga Ugo-Chinyeri ya ce hadakar da su kayi da jam’iyyar PDP a ranar Litinin ba maja ce da zata mayar da su a matsayin jam’iyya guda ba face dai wani yunkuri na sake hada kan Najeriya.

Mun shirya a daure mu ko mu mutu akan zaben 2019 – Shugaban jam’iyyar PDP

Mun shirya a daure mu ko mu mutu akan zaben 2019 – Shugaban jam’iyyar PDP

Ugo-Chinyeri ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Abuja cewa, hadakar tasu da akaiwa lakabi da Coalition for United Political Parties (CUPP) ya zo a daidai lokacin da ya dace inda jam’iyyu 39 suka hadu don ceto kasar nan.

Ya ce yunkurin ba kawai don su karbi gwamnati ba ne, amma har da hada kan Najeriya da kuma farfado da ita daga halin da take ciki. “Wannan ba maja ba ce, hadaka ce da ta kunshi jam’iyyu 389 cika har da babbar jam’iyyar adawa wato PDP. Munyi ne domin mu ceto kasarmu wacceke fama da matsalolin tattalin arziki da na siyasa iri-iri”.

KU KARANTA: 2019: Doyin Okube ya shawarci Saraki da ya tsaya takarar shugabancin kasa

Ugo-Chinyeri ya amsa cewa ba abu ne mai sauki ba harhada kan jam’iyyun a wannan lokacin, amma kuma abu ne da zai kawo sauyi ga jam’iyyun 39 da suka amince su tattara karfi da karfe don yin aiki tare.

Hadakar dai zata fitar da dan takara guda ne wanda zasu taru su marawa baya kuma duka za su sadaukar da komai don ganin sun samu nasara a zabe mai zuwa musamman na kujerar shugaban kasa. A cewarsa Ugo-Chinyeri.

Sannan ya cigaba a cewa wannan hadakar ta su na da bambamci da irin wadda aka yi a shekarar 2015, domin su tasu buri da dalilin da yasa aka yi ta a bayyana ne suke, kana ya kuma tabbatar da zasu baiwa matasa ‘yan shekara 18-35 kashi 25% na mukaman gwamnatinsu idan sunyi nasara.

Daga karshe Ugo ya bukaci ‘yan Najeriya da su garzaya su yi rijistar katin zabe domin samun damar jefa kuri’a a zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel