An kama wanda ya kashe Diyar tsohon mataimakin gwamnan Ondo

An kama wanda ya kashe Diyar tsohon mataimakin gwamnan Ondo

Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo sun kama wani mutum mai suna Adeyemi Alawo, data ke zargin shi da kashe diyar tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lasisi Oluboyo mai suna Khadija

An kama wanda ya kashe Diyar tsohon mataimakin gwamnan Ondo

An kama wanda ya kashe Diyar tsohon mataimakin gwamnan Ondo

Rundunar ‘yan sandan jihar Ondo sun kama wani mutum mai suna Adeyemi Alawo, data ke zargin shi da kashe diyar tsohon mataimakin gwamnan jihar Ondo, Lasisi Oluboyo mai suna Khadija.

DUBA WANNAN: An gina asibitin da za'a dinga duba yaran da aka yiwa fyade a jihar Zamfara

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Ondo, DSP Femi Joseph Femi shine ya bayyana cewa Adeyemi Alawo ya shigo hannunsu kuma suna yin iya bakin kokarin su wurin bincike akan lamarin. Sannan akwai yiwuwar kwamishinan ‘yan sandan jihar zai yiwa manema labarai bayani a yau Talatar nan.

Kakakin rundunar ‘yan sandan yace sun samu nasarar kamo Alawo ta bayanan da suka samu kuma sun gano cewa ya turbude Khadija a gidansa dake Akure bayan daya kasheta, amma daya fuskanci cewar gawarta na wari, sai ya aiki wani yaron sa ya samo mishi lega domin ya saka gawar tata a ciki.

Bayan rundunar ‘yan sandan sun kammala binciken su, za a mika shi kotu domin gurfanar dashi, haka kuma suna bin sawun wasu dake da hannu a cikin wannan aikin rashin imani.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel