An gina asibitin da za'a dinga duba yaran da aka yiwa fyade a jihar Zamfara

An gina asibitin da za'a dinga duba yaran da aka yiwa fyade a jihar Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara ta samar da wata cibiya da zata dinga kula da yara wadanda aka yiwa fyade

An gina asibitin da za'a dinga duba yaran da aka yiwa fyade a jihar Zamfara

An gina asibitin da za'a dinga duba yaran da aka yiwa fyade a jihar Zamfara

Gwamnatin jihar Zamfara ta samar da wata cibiya da zata dinga kula da yara wadanda aka yiwa fyade.

Kwamishinar kula da al'amuran mata da kananan yara Hajiya Bilkisu Bungudu itace ta bayyana hakan a wata tattaunawa da tayi da manema labarai a ranar Litinin dinnan a garin gusau babban birnin jihar.

DUBA WANNAN: An kama mutane 11 da hannu a kashe - kashen jihar Zamfara

Bungudu tace samar da wannan cibiya yana daga cikin kokari da jihar keyi wajen bawa kananan yara kariya a yankin.

An kafa wannan cibiya ne a asibitin mata da kananan yara na King Fahad dake Gusau.

"An samar da cibiyar ne tare da hadin gwiwar hukumar lafiya da kuma ta adalci don karfafa cibiyar.

"Duk da cewa bamu da matsaloli sosai akan fyade anan Zamfara, zamuyi amfani da rahotannin da muka samu daga wajen iyayen yara.

"Munayi wa marasa galihu da marayu rigista da kuma masu gudun hijira dake ciki sannan mu horar dasu don samun rayuwa mai inganci".

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel