An kashe 'yan ta'addar Boko Haram 15 a jihar Borno

An kashe 'yan ta'addar Boko Haram 15 a jihar Borno

Rundunar sojojin Najeriya mai taken 'Nigerian Army 7 Brigade' ta 3 a multinational Joint Task Force ta kai wani samame ranar Litinin dinnan inda suka kashe yan ta'addan Boko Haram guda 15 a Arege a jihar Borno

An kashe 'yan ta'addar Boko Haram 15 a jihar Borno

An kashe 'yan ta'addar Boko Haram 15 a jihar Borno

Rundunar sojojin Najeriya mai taken 'Nigerian Army 7 Brigade' ta 3 a multinational Joint Task Force ta kai wani samame ranar Litinin dinnan inda suka kashe yan ta'addan Boko Haram guda 15 a Arege a jihar Borno.

A wata takarda da Daraktan hulda da jama'a na sojojin, Birgediya Janar Texas Chukwu yasa hannu, yace abin haushi, lokacin gamon su da yan ta'addan, wasu sun tsere cikin daji amma da raunikan harbin bindiga a jikkunan su.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa tayi gargadi akan yada labaran karya

Ya tabbatar da cewa rundunar sun tsananta bincike don ganin sun kama yan ta'addan da suka tsere.

Rundunar sun samu makamai a wurin 'yan ta'addar, ciki kuwa hadda bindigar jirgin sama guda daya, da bindigogi masu kirar AK 47 guda 5 da wani inji bindiga mai haske guda daya.

Ya kara da cewa soja daya ya samu rauni a cikin su kuma yanzu haka yana karbar magani a asibitin sojoji.

Yayi kira ga mutane dasu sanar wa da jami'an tsaro duk wani abin zargi da suka gani domin kawo karshen ta'addanci.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel