Jam'iyyar APDA ta cire kanta daga cikin 'yan PDP

Jam'iyyar APDA ta cire kanta daga cikin 'yan PDP

Jam'iyyar Advanced Peoples Democratic Alliance (APDA) ta karyata rahoton masu watsa labarai da suke yada jita - jitar cewa tana maganar hadewa da jam'iyyar PDP domin zaben 2019 dake gabatowa

Jam'iyyar APDA ta cire kanta daga cikin 'yan PDP

Jam'iyyar APDA ta cire kanta daga cikin 'yan PDP

Jam'iyyar Advanced Peoples Democratic Alliance (APDA) ta karyata rahoton masu watsa labarai da suke yada jita - jitar cewa tana maganar hadewa da jam'iyyar PDP domin zaben 2019 dake gabatowa.

Sanarwar jam'iyyar ta fito a ranar Litinin dinnan ta bakin mai magana da yawun jam'iyyar, Mista Bayo Olumoko, ya bayyana rahoton a matsayin kanzon kurege sannan kuma maganar bata da tushe balle makama.

DUBA WANNAN: 2019: Matasan Arewa sunce basu yadda shugaba Buhari ya zarce ba

Yace rahoton kirkirarre ne da aka hada domin kaskantar da nagartar jam'iyyar ta APDA.

"A yanda rahoton masu yada labarai yace jam'iyyar ta APDA tana cikin jam'iyyu 45 da zasu hade da jam'iyyar PDP domin yakar jam'iyyar APC "

" Domin gujewa tantama, jam'iyyar APDA bata cikin jam'iyyun da zasu hade da jam'iyyar ta PDP kuma bata da wannan burin." inji mai magana da yawun jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel