Labari na musamman: Gwamnonin Arewa 3 da suke hanyan komawa PDP

Labari na musamman: Gwamnonin Arewa 3 da suke hanyan komawa PDP

Gwamnoni uku da aka zaba karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na hanyarsu na komawa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Yayinda ake sauraron sanatoci 30 da mambobin majalisan wakilai 70 su sauya sheka cikin makonni biyu masu zuwa kafin majalisar dokokin tarayya ta tafi hutun dogon zango.

Wadanda ake sa ran komawansu sune wadanda suka kafa sabuwar jam’iyya tasu wato sabuwar APC,R-APC. Yawancinsu tsaffin yan jam’iyyar PDP ne kafin suka koma APC a shekarar 2014.

Gwamnonin da ake jira sune gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed (Kwara), gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom (Benue) da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal.

“Akwai shirin da wasu gwamnonin APC ke yi da rashin sauya sheka sai sun tayar da hayaniya a jam’iyyar tukunna” Wani gwamna ya laburta.

KU KARANTA: ‘Yan uwa 2 sun fada tarkon masu garkuwa da mutane, an nemi Naira miliyan N15m kudin fansa

Shi dai gwamna Tambuwal ana hasashen yana shirin takarar kujeran shugaban kasa, shi kuma gwamna AbdulFatah Ahmed kuma yana shirin takarar kujeran majalisan dattawa a jihar.

Shi kuma gwamna Samuel Ortom ya samu tabbacin takaran kujeransa karkashin jam’iyyar PDP daga bakin Sanata David Mark. Biyo bayan rikicinsa da tsohon gwamnan jihar, Sanata George Akume.

Shi kuma shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, yana kwantan bauna ne tukun kafin ya bayyana nasa na sauya sheka sannan kuma na takaran kujeran shugaban kasa.

A yanzu haka jam’iyyar APC na da jihohi 24 yayinda PDP ke da 11 sannan jam’iyyar APGA da jiha 1.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel