APC za ta yi nasara a 2019, da R-APC ko babu su - Oshiomhole

APC za ta yi nasara a 2019, da R-APC ko babu su - Oshiomhole

Shugaban jam’iyyar APC na kasa ya ce jam’iyyar zata yi nasara a 2019 koda kuwa kungiyar aware na sabuwar APC ta balle.

Kungiyar R-APC wacce ta billo a makon da ya gabata na samun jagoranci daga Galadima, tsohon sakataren jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC).

Kungiyar wacce ta bayyana kanta a matsayin APC na “gaskiya” na da goyon bayan shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso, sannan kuma akwai sauran jiga-jigan APC da dama.

APC za ta yi nasara a 2019, da R-APC ko babu su - Oshiomhole

APC za ta yi nasara a 2019, da R-APC ko babu su - Oshiomhole

Mambobin kungiyar na R-APC, sun hada da mutanen jam’iyyu daban-daban da suka hade don kafa APC ciki harda CPC, ANPP da kuma N-PDP.

KU KARANTA KUMA: Mambobin R-APC na majalisar dokoki na shirin yiwa APC kankat a ranar 31 ga watan Yuli

Oshiomhole ya ce ya fara tattaunawa da mambobin kungiyar dake da korafi mai ma’ana, don haka za su iya share Buba Galadima.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel