Kotu ta umarci hukumar ‘yan sanda ta kama shugaban hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano

Kotu ta umarci hukumar ‘yan sanda ta kama shugaban hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano

A yau, Litinin, ne wata babbar kotu a Kano dake zamanta a karamar hukumar Gezawa ta bayar da umarnin kama Muhyi Magaji Rimingado, shugaban hukumar sauraron korafin jama'a da yaki da cin hanci ta jihar (KSPCA).

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewar, kotun ta bayar da umarnin kama Muhyi din ne bayan ya zarge ta da yiwa hukumarsa zagon kasa a yakin da take yi da cin hanci. Muhyi ya zargi kotun da taimakawa tsohoon babban akawun jihar Kano, Aisha Bello, a tuhumar da ake yi mata ta wawurar kudin jama’ar jihar Kano.

Saidai alkalin kotun, Jastis Muhammad Yahaya, a wata takarda mai lamba K/M235/2018 da ya aikewa mataimakin shugaban rundunar ‘yan sanda shiyya ta 1 ya bukaci hukumar ‘yan sanda ta kamo tare da kawo masa Muhyi gabansa kafin ranar 18 ga watan Yuli da muke ciki.

Kotu ta umarci hukumar ‘yan sanda ta kama shugaban hukumar yaki da cin hanci ta jihar Kano

Muhyi Magaji Rimingado; shugaban hukumar sauraron korafin jama'a da yaki da cin hanci ta jihar Kano

Kotun ta bayyana cewar ta dauki wannan mataki ne bayan Muhyi ya ki amsa gayyatar da tayi masa domin yi mata Karin bayani a kan wani korafi a kansa da wata mata, Hajiya Farida Tahir, ta shigar a kansa.

A bangare guda, hukumar sauraron korafin jama’a da yaki da cin hanci ta jihar Kano (KSPCA) ta bayyana cewar ta aike da takardar korafi a kan Jastis Yahaya zuwa ga hukumar kula da sashen ta kasa (NJC).

DUBA WANNAN: Badakalar cin hancin N15bn: Kotu ta tsayar da ranar yankewa Bafarawa hukunci

Rikici tsakanin Muhyi da Jastis Yahaya ya yi zafi sosai a satin day a gabata hart a kai ga kowanne bangare ya bayar da umarni a kamo masa abokin rikicinsa.

WAta majiya ta shaidawa Daily Nigerian cewar ba don gwamna Ganduje ya shiga tsakani bad a sai an bawa hammata iska tsakanin Muhyi da jastis yahaya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel