Ina matukar godiya ga PDP da amincewa da dawowanmu – Babban jigon R-APC

Ina matukar godiya ga PDP da amincewa da dawowanmu – Babban jigon R-APC

Shugaban nPDP kuma babban jigon R-APC, Abubakar Kawu Baraje ya nuna godiyarsa ga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) da amincewa da dawowansu jam’iyyar tare da mambobinsa.

Mr. Baraje, wanda abokine ga shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana hakan ne a yau Litinin a farfajiyar Shehu Yar’adua dake birnin tarayya Abuja inda PDP, R_APC, SDP da sauran jam’iyyu 30 suka taru domin yarjejeniya kan yadda zasu kada shugaba Buhari a 2019.

Kawu Baraje wanda tsohon shugaban PDP ne ya bayyana cewa shi da mabiyansa sun yi batan hanya ne a shekarar 2013 da suka bar PDP.

Mambobin nPDP da suka bar jam’iyyar APC dai har yanzu basu alanta fitarsu daga cikin jam’iyyar ba, bal sun kafa sabuwar kungiyar hamayya tasu a cikin APC da suna R-APC.

Mambobin R-APC din da ke taron sun kunshi shugabansu, Injiniya Buba Galadima; sanata Dino Melaye da sauransu.

Zaku tuna cewa wasu mambobin jam’iyyar APC sun bayyana niyyar fitarsu daga jam’iyyar bisa ga zalunci da bita da kullin da ake musu a cikin jam’iyyar.

Daga cikin wadanda suka bayyana hakan sune Sanata Shehu Sani, Buba Galadima, Bukola Saraki, Rabiu Kwankwaso da sauransu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel