Yanzu Yanzu 2019: R-APC, PDP da sauran jam’iyyu sun hadu, sun shiga yarjejeniya kan yadda za su ba Buhari kashi

Yanzu Yanzu 2019: R-APC, PDP da sauran jam’iyyu sun hadu, sun shiga yarjejeniya kan yadda za su ba Buhari kashi

Wasu shugabannin gamayyar jam’iyyar mai mulki, APC, a ranar Litinin sun hadu a Abuja domin jiga yarjejeniya da wasu jam’iyyun adawa kan zaben 2019.

Mambobin kungiyar sabuwar APC (R-APC) karkashin jagorancin shugabansu Buba Galadima sun halarci taron a ranar Litinin, 9 ga watan Yuli.

A makon day a gabata ne kungiyar sabuwar APC ta bayyana kanta. Ana ganin cewqa kungiyar na goyon bayan shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara ne.

Yanzu Yanzu 2019: R-APC, PDP da sauran jam’iyyu sun hadu, sun shiga yarjejeniya kan yadda za su ba Buhari kashi

Yanzu Yanzu 2019: R-APC, PDP da sauran jam’iyyu sun hadu, sun shiga yarjejeniya kan yadda za su ba Buhari kashi

Mambobin kungiyar na zargin jam’iyyar APC mai mulki da mayar da su saniyar ware.

Mista Galadima ya hadu da shugabannin jam’iyyun adawa irin su PDP da SDP domin sanya hannu a takardan fahimta.

KU KARANTA KUMA: Yadda Najeriya za ta ci gaba da dorewa – Obasanjo

Baya ga Mista Galadima, sauran mutanen da suka halarci taron sun hada day an PDP ciki harda mataimakin shugaban majalisar wakilai Ike Ekweremadu, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Sanata Dino Melaye da Gwamnan jihar Akwa Ibom, Emmanuel Udom.

Wani tsohon Sanata, Ben Obi wanda ya zanta da manema labarai ya ce jam’iyyun sun hadu ne domin shiga yarjejeniya kan yadda zasu kafa jam’iyyar da zata kwace mulki a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel