Yadda Najeriya za ta ci gaba da dorewa – Obasanjo

Yadda Najeriya za ta ci gaba da dorewa – Obasanjo

Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa hadin kan yan Najeriya ba abu ne da za’a yi masa rikon-sakainar-kashi ba, balle har wani ya shigo da son zuciyarsa ya bukaci sai an yi masa abin da ya ke so idan ana so a ci gaba da tafiya tare.

Obasanjo ya ja kunnen kafafen yada labarai da su guji yada abubbuwan da ka iya haddasa mummunan rikici a kasar.

Tsohon shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a ranar Asabar lokacin da ya zama mai masaukin baki a bikin shekara na Hukumar Gudanarwar Editocin Tsare-tsaren kamfanin Penpushing Media.

Yadda Najeriya za ta ci gaba da dorewa – Obasanjo

Yadda Najeriya za ta ci gaba da dorewa – Obasanjo

Ya ce sai ‘yan Najeriya sun riki kowani bangare na kasar nan a matsayin abokan gudu tare da tsira tare, sannan kasar nan za ta iya ci gaban da za a yi tinkaho da ita.

KU KARANTA KUMA: Muna da hujja akan yan siyasar dake da hannu a kashe-kashe – Fadar shugaban kasa

Ya ce bambancin kabilu da yaruka da addini wata albarka ce ga kasar nan, ba matsala ba ce.

Daga nan sai ya nuna takaicin sa matuka gaya a kan yadda jama’a da dama suka fara dawowa daga rakiyar gaskata kafafen yada labarai sosai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel