Ana jinya a Jihar Neja bayan mai ya kona wasu Bayin Allah

Ana jinya a Jihar Neja bayan mai ya kona wasu Bayin Allah

- Wani bututun man fetur ya fashe a cikin Jihar Neja kwanaki

- Hakan yayi sanadiyyar raunata mutane sama da 5 a nan-take

- Wasu da ke kokarin kalo fetur dai ba su ji da dadi ba a hadarin

Mun samu labari cewa wasu mutane sun kusa lekawa barzahu bayan da man fetur ya nemi yin sanadiyyar su zuwa lahira a wani Kauye da ake kira Dago-Pogo a cikin Jihar Neja. Hadarin ya kona gidaje da gonaki na Bayin Allah.

Kamar yadda labari ya zo mana kwanaki fetur yayi tsiya a Jihar Neja da ke Arewa maso Tsakiyar Najeriya inda wasu su ka kayi kokarin kalo man fetur da ya zube a wani kauye. Man ya zube ne bayan wani bututun fetur ya fashe.

KU KARANTA: Janar Buratai ya mika wasu 'Yan Boko Haram hannun UN

A baya da an rahoto cewa wasu sun mutu a wannan hadarin da ya barke. Daga baya dai mun gano cewa ba a rasa rai ba amma an jikkata kwarai inda akalla mutum 5ssu ka kone. Dole dai Jami’an kwana-kwana su ka kawo dauki nan-take.

Ana dai zargin wasu Tsagera ne su kayi kokarin sace man fetur daga wani bututun Kamfanin mai na kasa watau NNPC. Jami’an tsaro na NSCDC da kuma Hukumar bada agaji na gaggawa na Jihar Neja sun yi masa sun nufo inda abin ya faru.

Kun ji cewa Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da Jami’an shige da fice na kasar nan watau NIS cewa akwai wata sabuwar Kungiyar addinin Musulunci da ta shigo cikin Najeriya kuma ta ke daukar Mabiya a cikin Arewacin kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel