Karar kwana ta kai wani saurayi gamuwa da budurwar da ya hadu da ita a waya

Karar kwana ta kai wani saurayi gamuwa da budurwar da ya hadu da ita a waya

- Karar kwana ya sanya wani saurayi kaiwa budurwar da bai taba gani ba a zahiri ziyara

- Ziyarar da kuma ta zamo sandiyyar mutuwarsa bayan wasu mahara sun kai masa hari

A ranar Lahadin karshen makon da ya wuce ne jami'an yan sanda su ka bayyana yadda su ka gano gawar wani matashi a kusa da barikin sojoji da ke yankin Nkwoagu a karamar hukumar Abakalikin jihar Ebonyi.

An kashe wani Saurayi da ya kaiwa budurwarsa da suka hadu a waya ziyara a karon farko

An kashe wani Saurayi da ya kaiwa budurwarsa da suka hadu a waya ziyara a karon farko

Gawar mamacin wanda ba'a kai ga gano sunansa ba, amma an tabbatar da mutumin yankin Ishieke ne da ke karamar hukumar Ohaukwu ta jihar fatakwal.

Wata majiya ta bayyana cewa mamacin ya taho ne tun daga jihar fatakwal domin kawo ziyara gurin yarinyar da ya ke fatan ya aure ta, kuma majiyar ta kara da cewa wannan ne karon farko da ya kawo mata ziyara.

KU KARANTA: ‘Yan uwa 2 sun fada tarkon masu garkuwa da mutane, an nemi Naira miliyan N15m kudin fansa

Sai dai kawai gaisuwa da ke wanzuwa a tsakaninsu ta hanyar wayar sadarwa, bayan yazo gurin masoyiyar tasa ne inda ta ke da dan karamin shagon sayar da kayan masarufi da ke kusa da barikin sojojin, sai su ka rankaya gida inda a nan ne ya gamu da ajalinsa bayan da wasu mahara su kai masa hari.

Da ya ke tabbatar da faruwar al'amarin kakakin rundunar ‘yan sanda na kasa reshen jihar Ebonyi Loveth Odah, ya ce a ranar Lahadi ne suka sami gawar mamacin a yashe gab da barikin sojoji.

"Matashin ya zo gurin budurwarsa ne inda ya sameta a shagonta,bayan almuru yayi sai ya yi korafin cikin shagon sauro ya yi yawa, daga nan sai suka nufi gidan su yarinyar, inda akan hanyarsu ne suka hadu da wasu matasa guda 3, wadanda su ka boye fuskarsu da wani abu.

Nan take kuma matasan su ka far masa, inda su ka caka masa wuka, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarsa" in ji Loveth.

A karshe ya tabbatar da rundunar ‘yan sanda za ta yi iya bakin kokarinta, wajen gano wadanda su ka aikata wannan mummunan laifin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel