Muna da kwararan shaidu akan hannun 'yan siyasa a rikicin dake faruwa a kasar nan - Fadar Shugaban Kasa

Muna da kwararan shaidu akan hannun 'yan siyasa a rikicin dake faruwa a kasar nan - Fadar Shugaban Kasa

A ranar Lahadin nan ne fadar shugaban kasa tace ta samu kwararan shaidu da suke nuna hannun 'yan siyasa a kashe - kashen da ke faruwa a fadin kasar nan

Muna da kwararan shaidu akan hannun 'yan siyasa a rikicin dake faruwa a kasar nan - Fadar Shugaban Kasa

Muna da kwararan shaidu akan hannun 'yan siyasa a rikicin dake faruwa a kasar nan - Fadar Shugaban Kasa

A ranar Lahadin nan ne fadar shugaban kasa tace ta samu kwararan shaidu da suke nuna hannun 'yan siyasa a kashe - kashen da ke faruwa a fadin kasar nan, da kuma rikicin makiyaya da manoma. Fadar shugaban kasar tace 'yan siyasan suna amfani da 'yan ta'adda wurin kaddamar da ta'addancin su.

Babban mai bawa shugaban kasa shawara a bangaren yada labarai, Malam Garba Shehu, shine ya bayyana hakan jiya a Abuja.

DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa tayi gargadi akan yada labaran karya

"Kamar yanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana, yace akwai kwararan shaidu da suke nuna hannun wasu 'yan siyasa a rikice - rikicen dake faruwa a kasar nan.

"Matsalar canjin yanayi na damun kowacce kasa a duniyar nan, saboda haka zamu hada karfi da karfe da kasashen da makwabta domin kawo karshen ta'addanci a kasar nan.

A nashi bangaren Lauyan kare hakkin dan adam, Mista Femi Falana (SAN), ya bukaci gwamnatin tarayya data bayyana mutanen da suke da hannu a kashe - kashen dake faruwa a kasar nan domin gabatar da hukunci a kansu. Lauyan yace ya kai karar Babban Alkalin Alkalai na kasa Abubakar Malami, domin kotu ta takura su wurin fito da wadanda suke tada rikici a kasar nan. "Kamar yanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana, yace akwai kwararan shaidu da suke nuna hannun wasu 'yan siyasa a rikice - rikicen dake faruwa a kasar nan.

"Matsalar canjin yanayi na damun kowacce kasa a duniyar nan, saboda haka zamu hada karfi da karfe da kasashen da makwabta domin kawo karshen ta'addanci a kasar nan.

A nashi bangaren Lauyan kare hakkin dan adam, Mista Femi Falana (SAN), ya bukaci gwamnatin tarayya data bayyana mutanen da suke da hannu a kashe - kashen dake faruwa a kasar nan domin gabatar da hukunci a kansu. Lauyan yace ya kai karar Babban Alkalin Alkalai na kasa Abubakar Malami, domin kotu ta takura su wurin fito da wadanda suke tada rikici a kasar nan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel