Sauya sheka: Muna jiran umurni daga Saraki – Shugaban APC Kwara

Sauya sheka: Muna jiran umurni daga Saraki – Shugaban APC Kwara

Mambobin jam’iyyar APC a jihar Kwara sun ce suna jiran izini daga shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki kan ko su sauya sheka daga APC ko kuma kada da sauya.

Shugaban jam’iyyar, Hon. Ishola Balogun-Fulani, ya bayyana a wani taron manema labarai cewa mambobin jam’iyyar na tare da Saraki kuma za su bi hukuncin da ya yanke.

Balogun-Fulani ya bayyana APC a matsayin rusasshiyar jam’iyya, inda ya bayyana cewa hadin kai tsakanin mambobin jam’iyyar ya ruguje saboda shari’ar shugaban majalisar dattawa da aka yi ba bisa ka’ida ba.

Sauya sheka: Muna jiran umurni daga Saraki – Shugaban APC Kwara

Sauya sheka: Muna jiran umurni daga Saraki – Shugaban APC Kwara

An bukaci shugaban jam’iyyar da ya yi martani akan kiran da sanatocin jam’iyyar guda uku suka yi in da suka nemi Saraki ya zo ya jagorance su wajen fita daga APC. Shugabannin jam’iyyar uku na wajen taron a jiya yayinda Balogun-Fulani ya koro jawabi.

KU KARANTA KUMA: Muna da hujja akan yan siyasar dake da hannu a kashe-kashe – Fadar shugaban kasa

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnan jihar Kwara Abdulfatah Ahmed ya kuma sukar masu danganta shi da Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ga lamarin fashin da yayi sanadiyan rasa rayuka a Offa.

Gwamnan yayi Allah wadai da lamarin a lokacin wata hira a gidan tyalbijin din Channels a wani shirin siyasa na musamman da ake nunawa a ranar Litinin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel